Sabon kundin tsarin mulkin Masar

Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Sojin Masar ta zartar da wani daftari kan sauye sauyen da za'a yi wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda za'a gabartarwa jama'ar kasar domin samun amincewarsu .

Karkashin sauye sauyen da za'a gudanar, za'a amincewa shugaban kasar wa'adin shekaru hudu su biyu a maimakon shekaru shidda.

Shugaban kwamitin sharia na kasar Tariq Albishiri ya ce za'a kuma sake baiwa bangaren shariar kasar damar sa ido kan zabukan kasar.

Masu hammaya da gwamnatin kasar na bukatar ganin cewa an yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.