An fara kwashe yan Ghana daga Libya

Image caption Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills

Ministan harkokin wajen Ghana Mohammed Mumuni ya ce gwamnatin kasar ta fara kwashe yan kasarta daga Libya.

Ministan ya shaidawa BBC cewa an kwashe yan Ghana hamsin da biyar wadanda suka tsere zuwa iyakar Masar.

Ya kuma ce gwamnati na da anniyar ganin cewa ta kwashe yan kasar su kusan dubu hudu daga Libya.

Sai dai ya ce ba zai iya taimakawa dubun dubatar yan kasar dake Libya ta haramciyyar hanyar ba.

Mr Mumuni ya ce ana cikin matsanancin hali saboda yan kasar Libya sun rika yunkurin kaiwa bakar fata da dama hari bisa zargin da akeyi musu na mayyakan haya masu yiwa kwanel Gaddafi aiki.