Rikicin kasar Libya

Hakkin mallakar hoto AFP

Daya daga cikin 'yayan Shugaba Gaddafi Saif Al Islam ya yi gargadin boren da ake yi a Libya watakila ya kaiga rabuwar kasar abun da kuma zai janyo tashen tashen hankula na wani tsawon lokaci.

Ya ce kasar ba zata samu cigaba ba, idan har ba'a cimma matsaya kan sauye sauyen da za'a gudanar a harkar siyasar kasar ba.

Rahotannin baya bayan nan daga Tripoli babban birin kasar Libya , sun ce hankali ya dan kwanta a birnin.

Wani dan jarida a Libya ya shaidawa BBC cewa magoya bayan shugaba Gaddafi sun taru a dandalin Green a tsakiyyar birnin domin su nuna goyon bayansu ga shugaban kasar.