Jakadu a Geneva na tattaunawa a kan Libya

Ministoci daga kasashen duniya na wani taro a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva akan abubuwan dake faruwa a Libya.

Jakadun sun hallara ne domin taron Majalisar Dinkin Duniya akan hakkokin bil adama, sai dai za su yi amfani da damar wajen tattauna batun yawaitar tashe tashen hankulan dake faruwa a Arewacin nahiyar Afirka.

Cikin mahalartan har da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da Ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague, da takwaransa na Russia Sergei Lavrov da takwarorinsu na Italiya da Faransa da Jamus da Tunisia da kuma Turkiyya.

Abubuwan da za'a tattauna dai sun fi mahimmanci nesa ba kusa ba akan abubuwan da ke faruwa a hukumar dake rajin kare hakkokin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton za ta bukaci ministocin nahiyar turai da su fito da wasu hanyoyin bullowa badakalar dake faruwa a Libya, musamman ma bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya garkama nasa takunkumin akan Kasar.

Misis Clinton za ta bukaci a samu hadin kai a tsakanin Amurka da Birtaniya wajen ganin lallai Kanal Muammar Gaddafi ya sauka daga kan mulki cikin sauri.

Hillary Clinton za kuma ta gana da Jakadu daga kasashen dake yankin ciki har da Tunisia da Jordon.

Sannan wani batu da ka iya tasowa ma shine nahiyar Turai wadda kasar Italiya ke jagoranta, za ta duba yanda za'a bullowa masu neman mafakar siyasa daga Arewacin nahiyar Afirka zuwa nahiyar Turai.

Sannan kuma ma hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na iya maimaita kiran da ta yi akan nahiyar Turai da ta tausayawa duk wasu wadanda suka arce a sanadiyar tashin hankali.