Mata a Najeriya na kirafin rashin wakilci a zabe

Mata a Najeriya na korafin rashin samun wakilci a zabukan kasar da za'a yi nan ba da jimawa ba.

A yayin da ake tunkarar babban zabe a Najeriya, mata da dama na ganin har yanzu basu samu wakilcin da ya kamata a matakan gwamnatoci daban-daban ba, ko kuma ma a basu damar fitowa takara kamar mazaje, duk da irin gwagwarmayar da suke cewa sun dade suna yi a fagen siyasar Kasar.

Mata a Najeriya kamar sauran takwarorin su a wasu kasashen, sun jima suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban demokaradiyya.

Su kan bayar da gudumawa a wajen kada kuri'a, har ma a wajen fitowa yakin neman zabe domin tabbatar da cewar jam'iyar da suke marawa baya ta samu galaba.

Duk da cewar wasu matan na kokawa da irin yadda mazajen ke yi musu ka- ka- gida tare da nuna musu banbanci a fagen siyasa, wasu kuwa cewa suke matan basa hada kansu wajen marawa 'yan uwansu mata baya a wajen fitowa takarar.