Tarzoma ta barke a masarautar Oman

Akalla mutane biyu ne aka kashe a kasar Larabawa ta Oman, a lokacin da jami'an tsaro suka bude wuta a kan masu zanga-zangar da ke neman a yi sauye-sauyen siyasa.

An yi taho-mu-gaman ne a garin Sohar mai masana'antu, wanda ke arewa-maso-yammacin Muscat, babban birnin kasar.

An ce daruruwa mutane ne suka taru a can din a wuni na biyu.

An kuma ba da rahoton wata zanga-zangar a garin a kudancin kasar.

Jiya Asabar, Sultan Qaboos Bin Sa'id na Oman din, ya yi ma majalisar ministocinsa garambuwar, a wani yunkuri na saukaka rikicin.