An zargi Belarus da karya takunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe sun ce Ouattara ne ya lashe zaben

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon, ya zargi Kasar Belarus da karya takunkumin hana sayar da makaman da aka sanyawa Kasar Kot D'voir, tun shekara ta 2004.

Kakakin Mr Ban Ki Moon, ya ce kasar ta Belarus ta tura wasu Helikoftoci guda ukku zuwa ga rundunar sojojin kasar Cot D'voire wadda ke karkashin ikon Laurent Gbagbo, mutumin da yayi mirsisi akan karagar mulki bayan kayen da ya sha a zaben watan Nuwambar bara.

Kasar ta belarus dai ta fitar da wata sanarwa tana musanta shigar da makamai zuwa kasar ta Kot devuwa.