An bude taron neman zaman lafiya a Somalia

Shugaban Somalia
Image caption Ya yi kira mai sosa rai na neman zaman lafiya

A yau ne a birnin Accra a kasar Ghana aka fara wani taron yini uku don duba hanyoyin samar da zaman lafiya a kasar Somalia.

Mahalarta taron dai sun hada da membobin gwamnatin rikon kwaryar kasar, da 'yan majalisun dokokin da sauran masu fada a ji na Somaliar.

Akwai kuma babban jakadan kungiyar tarayyan Afrika kan matsalar Somalian, wato tsohon shugaban kasar, Ghana Jerry Rawlings.

Shugaban Ghanan mai ci wato John Atta Mills shi ya jagoranci bikin bude taron.

Ya kuma jaddada bukatar da ake da ita ta samun zaman lafiya.

Shi ma shugaban gwamnatin rikon-kwarya ta Somaliyar, kira ya yi ga kasashen Afrika da su taimaka masu a sami zaman lafiya a kasar ta Somalia.