Tsarin kafa Hukumar Zabe da ayyukanta

INEC
Image caption Akwai babban kalubale a gaban shugabannin hukumar na ganin sun bi dokoki sau da kafa

Sashi na 153 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya kafa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a matsayin wata Hukuma ta din-din-din, da za ta iya karar wasu, ita ma kuma za'a iya kararta.

Baya da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya dorawa Hukumar, Hukmar na da karfi wajen gudanar da:

· Wayar da kan masu jefa kuri'a da ilmantar da su kan nauyin da ke kansu. · Inganta ilmin jama'a bisa gudanar da sahihin zabe na dimokradiyya. · Gudanar da zaben raba gardama idan bukatar hakan ta taso bisa kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ko bisa kowace doka ko kuma dokar Majalisar dokoki ta kasa.

6-(1) Dokar kafa Hukumar zaben ta ce a kafa Humukar a duk jahohin kasar da ma babban birnin tarayya, wacce za ta gudanar da duk aikin da hedkwatar hukumar ta kasa za ta sa ta daga lokaci zuwa lokaci.

(2) Ayyukan da mutumin da aka zaba zai shugabanci ofishin Hukumar na jihohi sun hada da:

(a): Zai kasance a karkashin hukumar ta kasa.

(b): Zai rike ofishin har na tsawon shekaru biyar.

(3); Shugaban kasa ne kadai zai iya cire shugaban Hukumar zaben bisa bayanan kashi biyu cikin uku na Majalisar dattawa na cewa baya gudanar da aikin da ya kamata ko kuma aikata abinda bai dace ba.

Nadin Shugabannin Hukumar Zabe

11. (1) Tilas ne Hukumar ta nada jami'an da za su kula da aikin rijistar zabe wadanda ba 'yan jam'iyyun siyasa ba.

(2) Kowane mutum na iya nuna kin amincewarsa da duk wani ma'aikacin hukumar a lokacin rajistar, muddin rashin bayyana korafinsa na iya yin illa ga aikin rijistar.

(3) A karkashin sashi na daya na wannan dokar tilas ne jami'an da aka su tafiyar da aikinsu bisa tsarin hukumar zaben, kuma ba wani mutum ko hukuma da za tai iko da su bisa aikinsu, in banda hukumar zaben.