Wasu sassan kundin dokar zabe

Inec
Image caption Aikin Hukumar zabe ne na ta tattara ta kuma ci gaba da sabunta rijistar masu zabe

(1) Aikin Hukumar zabe ne na ta tattara ta kuma ci gaba da sabunta rijistar masu zabe a koda yaushe bisa dokar rijistar masu zabe, wadda za ta kunshi sunayen mutanan da suka cancanci zabe a kowane mataki.

(2) Ya kamata hukumar ta kasance tana da rajistar masu kada kuri'a na dukkan jihohin kasar hadi da babban birnin tarayya, a matsayin wani bangare na rajistar masu zabe.

(3) Ya kamata hukumar zabe ta kasance tana da rajistar masu kada kuri'a a dukkan kananan hukumomin jihohin kasar har da na babban birnin tarayya.

(4) Tilas ne rajistar ta kunshi duk bayanan masu zabe da ake bukata a takardun da hukumar ta bayar a cike.

(5) A karkashin wannan dokar tilas ne a kammala rjistar masu kada kuri'a kwanaki 60 (wata biyu) gabanin a gudanar da kowane zabe.

(6) Tilas ne a gudanar da rijistar masu kada kuri'a a wuraren da Hukumar ta samar domin aikin.

10. -(1) Za'a iya ci gaba da rajistar dukkan wadanda suka cancanci kada kuri'a ba tare da an yi illa ga sashi na 10 sakin layi na 5 na dokar zaben.

(2) Tilas ne wanda zai yi rajista bayan lokacin da aka diba ya wuce ya bayyana da kansa a wajen da ake rajistar da daya daga cikin wadannan abubuwan:

(a) Takaddar shaidar haihuwa

(b) Katin shaidar dan kasa ko lasisin tuki; ko kuma

(c) duk wasu bayanai da za su tabbatar da kasarsa da shekarunsa.

(3) Tilas ne cikin kwanaki 60 kowacce shekara hukumar zaben ta bawa jam'iyyun siyasa sunaye da adireshin duk wanda akaiwa rajista a wannan shekarar.

(4) Idan hukumar zabe ta sanar da lokacin da za'a gudanar da zabe a karkashin sashi na 31 na wannan dokar, to da rijistar da ake da ita ne masu zabe za su yi amfani wajen kada kuri'arsu.

(5) Da wannan rijistar ce za ayi amfani wajen zabukan cike gurbi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

(6) Da zarar an magance duk wasu korafe-korafe da ka iya tasowa ko kuma wa'adin da aka diba masa ya cika, tilasne a sa sunayen a sabuwar rajistar da aka sake, wadda hukumar zaben za ta tabbatar da ingancinta a matsayin rajistar.

Cancantar yin rajista

12.-(1) Mutum zai cancanci yin rajista ne idan:

(a) Shi / Ita dan Najeriya ne / ce.

(b) Ya cika shekaru 18 da haihuwa.

(c) Tilasle ace yana zaune ko aiki a kusa da unguwa / Karamar Hukamar da ake gudanar da aikin rijistar.

(d) Ya kai kansa wajen da jami'an Hukumar zaben ke rijistar masu kada kuri'a.

(e) Ya kasance ba shi da wani laifi da kowace irin doka ta hana shi yin zabe a Najeriya.

(2) Ba bu wanda zai yi rijista a sama da wuri daya da ake gudanar da rijistar zaben ko kuma ya yi rijistar sunansa sama da daya a wurin rajista daya.

(3) Duk wanda ya saba sakin layi na biyu na wannan dokar ya aikata laifin da za'a ci shi tarar naira 100,000 ko hukuncin daurin da bai wuce shekara daya a gidan kaso ba ko kuma ma duka hukuncin biyu.

13. (1) Mutumin da ya tashi daga mazabar da ya yi rijista ya koma wata, zai iya neman kwamishinan zabe na wannan wajen da ya maida sunansa a cikin rijistar wadanda sukai taransifa ta wannan mazaba.

(2) A karkashin wannan dokar mutumin da ya nemi ai taransifar sunansa zai bada katin rijistar da akai masa a waccan mazabar, cikin kwanaki 30 kafin a gudanar da zabe a mazabar da ya koma.

(3) A karkashin dokar kwamishinan zaben zai tabbatar da cewa wannan mutumin na zaune a kusa da inda za a yi zabe a mazabar da ya koma kuma lallai ai masa rijista a mazabar da ya baro, kafin ya shigar da sunansa cikin sunayen 'yan taransifa.

Taransifar sunayen masu zaben da suka yi rajista

(4) Duk lokacin da jami'in zabe ya sa sunan mutum a cikin jerin sunayen 'yan taransifa a mazabarsa bisa umarnin kwamishinan zaben wajen, tilas ne:

(a) Ya sa sunansa a wata mazaba ko kuma rumfar zaben dake mazabarsa, ya kuma rubuta inda aka sa sunan na sa.

(b) Ya ba mutumin sabon katin zabe ka na kuma ya karbi tsohon dake wajensa.

(c) Ya tura kwafin rijistar ga jami'in zaben na mazabar da ya baro, shi kuma da zarra ya samu sai ya cire sunan mutumin daga rijistar mazabar.