Ana gwabza fada a birnin Misrata na Libya

Libya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Jama'a na ci gaba da kaurace wa kasar ta Libya

Rahotanni daga Libya sun ce ana gwabza kazamin fada tsakanin masu adawa da Kanal Gaddafi da masu goyan bayansa a garin Misrata.

Garin na Misrati dai na da nisan kilo mita dari biyu ta Gabashin Tripoli.

Wadanda suka ganewa idanunsu abinda ya faru sun ce an tabka fada a kewayen garin da filin saukar jiragen samansa.

Wani likita dake wajen ya shaida wa BBC cewa jiragen sama masu saukar angulu mallakar gwamnati ne suka kai hari kan wani gidan radio da masu zanga-zanga suka kafa.

Akwai rahoton da ke cewa masu goyon bayan shugaba Gaddafi sun yi wa garin Zawiya kawanya, a wani kokari na sake kwace shi bayan da ya kufce daga hannunsu.

Wakilin BBC a Tripoli ya ce wasu mutane na gudanar da zanga-zanga a wani sashi na birnin. Har yanzu dai birnin na hannun magoya bayan shugaba Gaddafi.

Karin bayani