Shugabannin yamma na tattauna mataki a kan Libya

Shugaba Gaddafi na Libya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yi wa kasar kofar raggo

Shugabannin kasashen yammacin duniya suna ta tattaunawa a kan hanyoyin matsin lambar da za su kara dauka a kan shugaban kasar Libya, Kanal Muammar Gaddafi, na ya daina sawa ana kashe mutanansa da ke nuna adawarsu da shi, kuma su shawo kansa na ya sauka daga kan mulki.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce zamu su gaba da duba dukkan hanyoyin da suka dace su dauka.

Ita ma kasar Faransa ta ce tana duba yiwuwar daukar matakin soji, yayin da shi kuma Firaministan Birtaniya David Cameron ke daga cikin wadanda ke aiki kan shirin hana jiragen saman libya tashi a sararin samaniyar kasar ta Libya.

Akalla mutane dubu daya ne ke ci gaba da isa kan iyakar Libya da Tunis cikin kowace sa'a, a kokarin guje wa rikicin da ake a Libya.

Baki daya tsawon ranar litinin, ma'aikata 'yan cirani daga kasashen Masar da sauran kasashe irin su Bangladesh na ta tuttuda zuwa kan iyakar, suna tarar da dubban 'yan uwansu da tuni suka kai wajen.

Kasashe na ta shirye-shiryen kwashe 'yan kasashensu da suka samu tserowa daga Libyan

Rahotanni daga Libya sun ce yau an gwabza kazamin fada tsakanin magoya bayan gwamnati da masu gaba da ita a garin Misrata, mai nisan kilomita dari biyu gabas da Turabulus, babban birnin kasar ta Libya.

Wani likita a birnin Misratan yace da misalin karfe hudu na safiyar yau, mukaji jirage masu saukar angulu na shawagi a sararin samaniyar birnin, kuma muna ji ana ta ruwan bama-bamai ana ta harbe harbe.

Rahotanni sun ce garin na karkashin ikon masu gaba da gwamnati ne, amma sauran kewayensa dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi ne ke rike da shi.