Za a maida wuta a Zaria bayan zanga-zanga

Tutar Najeriya
Image caption Suna kuma jiran samun ruwa

Gwamnan jihar Kaduna ta ba da umurnin maida wutar lantarki a garin Zaria ba tare da bata lokaci ba, bayan zanga-zangar da mutanen wani yanki na Zariyar suka yi.

Wasu mutane masu yawan gaske sun gudanar da zanga-zangar a yau a Zariar, inda suke bayyana korafinsu a kan abubuwa da dama da suka hada da rashin wutar lantarki da ruwan sha da kuma magunguna a asibitoci.

Dama dai garin na Zaria ya dade yana fama da karancin ruwan famfo, inda gwamnatocin jihar da dama suka sha yin alkawurran warware matsalar ba tare da cikawa ba.

Gwamnatin jahar kaduna ta mayar da martani dangane da zanga-zangar da aka gudanar yau a Zaria, domin nuna damuwa a bisa karancin wutar lantarki da katrancin ruwan famfo a garin na Zaria na wani dogon lokaci.