Dambarwa tsakanin PDP da CPC a Naija

A Najeriya, wata rigima ce ke neman kaurewa a tsakanin gwamnatin Jihar Naija, wadda jam`iyyar PDP ta kafa da kuma reshen Jihar na jam`iyyar adawa ta CPC.

Jam`iyyar CPC dai ta nemi izinin amfani da dandalin baje-kolin Jihar ne da ke Minna don kaddamar da yakin neman zaben dan takarar ta na shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari, amma gwamnati ta ce wasu sun rigata.

Sai dai jam`iyyar CPC ta yi zargin cewa gwamnatin na nema ta hana mata filin ne kawai saboda hamayya.

Jam'iyyar CPC ta kuma jaddada cewa lallai sai ta yi bikin a dandalin, a ranar uku ga watan Maris na wannan shekarar.