Amurka na ci gaba da sakawa Gaddafi matsin lamba

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin shugaba Barack Obama ta ci gaba da yin kira ga shugaban kasar Libya da ya sauka daga mulki, musamman ma bayan wata hira da ya yi da BBC da kuma tashar ABC ta Amurka.

Jakadar Amurkan a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sam Kanal Gaddafi bai cancanci ya ci gaba da mulki ba.

Ta dai bayyana shi ne a matsayin mutumin da bashi da hangen nesa.

Musamman a yanzu da aka kwashe mafi yawan 'yan Amurka daga Libya, gwamnatin Obama za ta ci gaba da matsa kaimi wajen sakawa Kanal Gaddafi matsin lambar sauka daga mulki.

Wannan dai wani martani ne da jakadar Amurka a majalisar dinkin duniya Susan Rice ta mayar akan jawabin da Shugaba Gaddafin ya yi.

Ta dai bayyana cewa idan har zai dinga magana da manema labaran Amurka da na kasashen duniya yana dariya, alhali ana kashe mutane a kasar sa, wannan ya tabbatar da cewa sam bai cancanci ya ci gaba da mulki ba.

Gwamnatin Amurkan dai na fatan cewa takunkumin da aka garkama zai fara yi wa Kanal Gaddafi ciwo, tare kuma da taimakawa wajen haddasa masa bakin jini a bangaren magoya bayansa.

Amurka ta saka masa haramci akan taba kadarorinsa da suka doshi dala biliyan talatin dake ajiye a kasarta, wanda kuma wannan shine haramci mafi girma da kasar ta taba sakawa.

Sannan kuma Amurka ta bayyana cewa zata sake matsawa da jiragen yaki na ruwa da na sama kusa da Libyan domin takaita shige da fice a kasar.

Sai dai kawo yanzu babu tabbacin cewa wannan zai samu amincewar kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.