Kimanin mutane Talatin sun ji rauni a Katsina

A Najeriya rahotanni daga Jihar Katsina sun ce kimanin mutane talatin ne suka samu munanan raunuka a yayin da suke gudun ceton rayukkansu.

Wannan dai ya faru ne a lokacin da 'yan sanda masu kare lafiyar Gwamnan Jihar suka rin ka harba bindigogi a sama da barkonon tsohuwa da nufin tarwatsa magoya bayan jam'iyyar CPC.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da 'yan jam'iyyar CPC suka yi dafifi a kan hanyar Katsina zuwa Kano suna ban-kwana da dan takarar Gwamna na Jam'iyyar ta CPC Sanata Lado Dan-Marke wanda ya yi taron gangami a birnin Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan dake tare da Sanata Dan-Marke sun rika cewa "Ba ma so, karya ne" a lokacin da Gwamnan Ibrahim Shehu Shema ke wucewa.

Lamarin da wasu da suka shaida lamarin suka ce mai yiwuwa ya harzuka masu kare lafiyar Gwamna Shema.

To, sai dai Gwamnatin Jihar Katsina na ganin laifin na 'yan CPC ne, inda Jami'in hulda da Jama'a na Gwamna Shema ya ce magoya bayan CPC ne suka rinka jifan su da duwatsu, har ma sun rotse motoci uku na Gwamnatin Jihar.