Amurka ta tura jiragen ruwan yaki Libya

Sakataren harkokin tsaron Amurka Robert Gates ya yi gargadin tsauraran matakan sojin da ka iya biyo baya a Libya, wanda zai iya hana shige da fice daga kasar.

Ya dai yi wannan jawabin ne a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi akan karin sojojin da aka tura kewayen Libya.

Mista Robert Gates ya bayar da odar turawa da jiragen ruwan yaki biyu dake dauke da jiragen helikoptoci da daruruwan sojojin ruwa zuwa yankin tekun Mediterranean, domin amfani dasu wajen aikewa da agaji kasar.

A wurin wani taron manema labarai da ya yi a ma'aikatar tsaron ta Pentagon ya bayyana cewa sojojin Amurkan ba za su yi wani abu da ya zarta hakan ba a kasar ta Libya.

Amurka na taka tsan tsan da batun garkama takunkumin hana shige da fice daga Libya.

Mista Gates ya kara ne da cewa kudurin Majalisar Dinkin Duniya na baya bayan nan bai bayar da damar amfani da matakin soji ba.

Matsayar da Kasar Russia ta dauka a yayin taron Majalisar Dinkin Duniyar, na fitowa fili ta bayyana cewa sam ba za ta amince da amfani da sojoji wajen hana shige da fice ba, ya sa lamarin da wuya ya yiwu.

Duk da son da Amurka ke yi na shiga cikin lamarin dake faruwa a Libya dai, ala tilas akwai inda dole ta ja birki.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka dai ta bayyanawa Sanatocin Amurka a yayin wani zaman Majalisa kan cewa Libya na iya nasarar samun demokradiyyar zaman lafiya, ko kuma ta tsunduma cikin yakin basasa.