'Yan jarida a Najeriya sun kalubalanci Sanata Aji

A Najeriya uwar kungiyar `yan jarida ta kasa ta yi Allah- Wadai da furucin da mai baiwa Shugaban Kasa shawara a kan ayyukan `yan majalisa, Sanata Abba Aji ya yi.

Shi dai Sanata Aji ya soki kokarin da `yan majalisun dokokin kasar ke yi na zartar da dokar da za ta tilasta wa Jami`ai da ma`aikatun gwamnati bai wa `yan jarida bayanai.

Kungiyar ta ce kamata ya yi Shugaba Goodluck Jonathan ya sallami mai ba shi shawarar daga aiki, saboda zai bata wa gwamnati suna.

Sai dai shi Sanata Abba Aji ya kafa hujjar cewa zartar da dokar na da hadari, saboda gwamnati za ta kasance ba ta da sirri.