Buhari ya kaddamar da kamfe a Kaduna

Image caption Janar Muhammadu Buhari

A Najeriya, dan takarar Shugaban kasa ta jam'iyyar CPC Janar Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfen din neman zaben sa a jihar Kaduna.

Dan takarar dai zai kaddamar da kamfe din sa a Minna jihar Niger a gobe alhamis, abun da kuma Hukumar 'yan sandan jihar ta hana.

Hukumar 'yan sandan ta ce akwai wani dan takarar wata jam'iyya da aka bawa izini ya yi taro a jihar domin haka bazata iya tabbatar da tsaron 'yan 'yan jam'iyyar CPC ba.

Jam'iyyar ta CPC dai ta ce za ta gudanarda da taron nata a Minna duk da cewa dai hukumar 'yan sandan jihar ta hana mata izini.

Wannan ne dai karon farko da jama'iyar za ta fafata a zaben game gari na Najeriyar, tun bayan da aka kirkiro ta yan watanni da suka gabata.

Sai dai wannan ne karo na ukku da dan takarar nata na Shugaban kasa yake takarar Shugaban Najeriya.

A baya dai yayi takarar ne a karkashin inuwar Jama'iyar adawa ta ANPP, kafin su raba gari da ita.