An sace sojojin kundunbala na Holand a Libya

Boren kasar Libya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Rikicin kasar ta Libya ya ritsa da 'yan kasashen waje da dama

Kasar Netherlands wato Holand, ta tabbatar da cewa an sace sojanta na kundunbala su uku, kuma an tsare su a kasar Libya.

Su dai sojan na Netherlands uku an kama su ne yayin da suke kokarin ceto wani dan kasarsu da kuma wani dan wata kasar Turai da masu dauke da makamai dake goyon bayan Kanar Gaddafi suka tsare a garin Sirte.

Wakilin BBC a Libya, ya ce yana da wuya a tantance matsayin harkokin tsaro da na soja suke a Libya yazu haka.

A bangare guda kuma kasashen duniya na ci gaba da kokarin kwashe wadanda suka tsallake daga kan iyakar kasar da Tunisia.

Cikin 'yan kwanakin dake tafe dai ana sa ran cewa, za'a kwashe 'yan cirani dubu shida 'yan kasar Masar zuwa birnin Alkahira.

Tuni dai kasashen Burtaniya da Faransa suka fara cika alkawarin da suka dauka na taimakawa wajen kwashe 'yan gudun hijirar.