Yiwuwar hana jirage tashi a Libya

Yiwuwar hana jirage tashi a Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu magoya bayan Gaddafi na murnar samun nasara

Kasashen kungiyar kawance ta NATO da kuma kungiyar kasashen Larabawa na duba yiwuwar nemo hanyoyin hana sojojin Kanar Gaddafi ci gaba da kai hare-hare a Libya.

Akwai dai tunanin sanya takunkumin tashi da saukar jiragen sama domin kare 'yan tawaye da kuma fararen hula a Libyan.

Sai dai matakin wanda aka fara tattauna wa a bayan fage a Majalisar Dinkin Duniya na da hadari.

Wakiliyar BBC Babara Plett ta ce, batun hana tashi da saukar jirage na daga cikin abubuwan da ake kamun kafa a kai.

Sai dai babu wata bukata da aka gabatar a hukumance a cewar wani jami'in diflomasiyya na kasashen Yamma.

'Ana nuna damuwa'

Wasu wakilan kwamitin tsaron irinsu Rasha na nuna damuwa, saboda matakin na hadari musamman ta fuskar siyasa.

Ra'ayin jama'a a Majalisar dai shi ne, irin wannan mataki na bukatar ganin an kai mummunan hari ta sama ga fararen hula, koda hakan ma ta faru, sai kasashen yankin sun amince tukunna.

Tuni dai kasashen Larabawa suka ce za su iya amince wa da dokar hana zirga-zirgar jiragen sama tare da hadin guiwar kungiyar Tarayyar Afrika idan lamarin ya ci gaba da munana.

Shi ma dai Sakataren tsaro na Amurka Robert Gates, ya nuna shakku kan matakin, yana mai cewa lamarin ba karamin aiki ba ne, don haka akwai bukatar taka-tsantsan.

A yanzu dai kasashen na Larabawa sun bar kofarsu a bude inda suke bayyana damuwarsu, matsayin da ba shi da wani banbanci da na kwamitin sulhun Majalisar ta Dinkin Duniya.