Za a kafa sababbin jami'o'i a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption An dade ana sukar yadda harkokin ilimi ke tafiya a Najeriya

A Najeria, Majalisar Zartawar kasar ta amince da baiwa wasu lasisin kafa jami'o'i masu-zaman-kansu guda hudu a wasu bangarorin kasar, cikinsu har birnin Abuja.

A kwanakin baya ma Majalisar ta amince za ta kafa wasu sababbin jami'o'i guda tara a wasu jihohin kasar.

Sai dai lamarin ya janyo mata suka daga Kungiyar Malaman Jami'o'i ta kasar, wadda ta ce gwamnati na nema ta cusa siyasa a harkar karatun jami'a.

Amma ministan ilimi ta kasar Farfesa Rukayya Ahmed Rufa'i, ta shaida wa wakilin BBC Ibrahim Isa, cewa matakin na su zai inganta fannin ilimi a kasar.

Yanzu dai jamillar jami'o'in a Najeriya sun kai dari da goma sha bakwai idan aka hada yawan jami'o'in gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma masu-zaman-kansu.