An tuhumi wani mutum da laifin lalata da 'ya 'yansa a Niger

Nijar Hakkin mallakar hoto AP

A jamhuriyar Nijar wani mutum ya bayyana a gaban kuliya bisa zargin yin lalata da 'ya 'yansa mata.

Hakan ya biyo bayan wani zargi ne da wata kungiyar kare hakkin mata da yara kanana a Nijar, ta yi na cewar mutumin-- wanda ba a bayyana sunansa ba, ya shafe shekaru tara yana tarawa da 'ya 'yan nasa, kuma ma har ya haifi 'Yaya 4 da su.

Tuni kotu ta saurari bahasi daga 'ya 'yan mutumin da kuma uwargidansa.

A yanzu haka ana dai ci gaba da tsare mutumin a gidan yari na Birnin Yamai.

Mutumin dai ya musanta zargin da ake yi masa.

Wannan al'amari dai ya zo ne a daidai lokacin da ake takaddama kan maganar kundin kare hakkin mata da kananan yara a kasar ta Nijar.