Gwamnatin Nijar ta ce ta na shirin kwaso 'yan kasarta daga Libya

Salou Djibo
Image caption Shugaban sojin Nijar

Gwamnatin Nijar ta bayyana cewar tana cikin shirin daukar matakin kwaso yan kasarta da suka makale a Libya.

Yan Nijar da dama ne dai suke ta kira ga gwamnatin kasar da ta yi kokarin samun yadda zata buda musu hanya daga Tripoli domin su koma gida.

Saidai kuma gwamnatin ba ta bayar da wani lokaci takamaimai ba na kwaso 'yan Nijar din da fadan da ake yi a Libyar ya rutsa da su.

A halin da ake ciki dai dakaru masu hamayya da Shugaba Gaddafi a Libyar sun karbe iko da brinin Brega mai tashar jiragen ruwa da ke gabashin kasar.

Hakan ya biyo bayan wani fada aka yi tsakanin sojoji masu biyayya ga Shugaba Gaddafi da kuma masu hamayya da shi.

A bangare guda kuma kotun tuhumar manyan laifuka ta Duniya ta ce za ta soma bincike game da yiwuwar aikata manyan laifuka a kan bil Adama a kasar ta Libya.