'Yan kwadago na fatan kawo sauyi a Najeriya

Zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zaben 2011 na da matukar mahimmanci ga tsarin dimokradiyya a Najeriya

A Najeriya, kungiyoyin kwadago sun sha alwashin taka mahimmiyar rawa wajen wajen bunkasa tsarin mulkin demukradiyyar a kasar.

Dama dai kungiyoyin kwadagon kan bada gudummawa wajen gudanar da harkokin zabe, inda suke gudanar da aikace-aikacen wucin gadi, da kuma sa ido akan yadda ake gudunar da zububbuka.

Sai dai ana zargin wasu ma'aikata da hada kai ta 'yan siyasa wajen magudin zabe a lokacin da aka ba su aikin gudanar da zaben, a cewar wakilin BBC a Abuja Yusuf Tijjani.

Amma shugabannin kungiyar kwadagon sun lashi takofin kawo karshen wannan dabi'a, suna masu cewa ba duka aka taru aka zama daya ba.

'Ba tare da an yi magudi ba'

A cewar Marwan Mustafa Adamu Sakataren kungiyar Ma'aikatan Kotu, za su tabbar da cewa zaben Najeriyar na bana ya zama abin koyi ga sauran kasashe.

"Za mu shiga cikin kungiyoyin da ke sa ido wahen harkokin zabe domin ganin cewa duk kuri'ar da aka kada ta yi tasiri, ba tare da an yi magudi ba".

Ya kara da cewa kungiyar kwadago ta taka rawa wajen tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a Hukumar Zabe ta Kasa INEC.

"Kuma muna saran shugabancin Hukumar na yanzu zai yi aiki cikin adalci da kamar yadda aka yi hasashe", a cewar Marwan Mustafa Adamu.