ACN ta kaddamar da kamfen din Shugaban kasa a Jigawa

Dubban magoya bayan jam'iyyar ACN ne suka halarci taron kamfe din dan takarar Shugaban kasar ta, Mallam Nuhu Ribadu, wadda aka yi a dandalin Aminu Kano dake birnin Dutsen jihar Jigawa.

An dai kaddamar da kamfen din ne na jihohin da ke arewa masu yammacin kasar, wanda suka hada da jihohin Kano da Katsina da Jigawa da Sokoto da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna.

Da yake gabatar da dan takarar shugaban kasar da mataimakinsa, Shugaban Jam'iyyar ACN Cif Bisi Akande ya ce 'yan takarar za su magance matsalolin Najeriya da nufin fidda ta daga halin da take ciki.

Ya ce Jam'iyyar za ta fi mayar da hankali ne a wajen magance rashawa da tabarbarewar tsaro da kuma talauci.

"Malam Ribadu Sananne ne a hakar tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa, kuma mataimakinsa Adeola ya kware wajen inganta harkar tattalin arzikin kasa, ina da kwarin gwiwa cewa su biyu za su magance matsalolin Najeriya." In ji Cif Akande.

Cif Akande ya ce 'yan takarar biyu za su samar da shugabancin da Najeriya ke bukata ganin cewa suna da sauran jini a jika, kuma sun lakanci dabaru na zamani.

Jam'iyyar ACN dai ita ce mafi girma a yanzu a jam'iyyun adawa a Najeriya inda take da gwamnoni 4 daga cikin 36 na kasar.