Fada da gudun hijira a Cote d'Voire

Alasanne Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ga alama an soma yakin basasa

Jamian Majalisar Dinkin Duniya a Code d'Voire sun ce mutane fiye da dubu dari biyu ne suka tsere daga wata anguwa d ake Abijan, babban birnin kasar, bayan da aka shafe wasu kwanaki ana mumunan fada.

'yan sanda dake biyayya ga Laurent Gbagbo, mutumin da yaki sauka daga kan karagar mulki bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar, da kuma ake takkadama a kai, sun yi taho mu gama da magoya bayan abokin hamayyarsa, Alasane Ouatara a anguwar Abobo.

Daga bisani a yau, jami'an tsaro sun kashe akala mata shidda wadanda ke jerin gwanon nuna goyon baya ga Mr Ouattara.

Helene Caux, jamia'a ce a hukumar kula da 'yan hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Code d'Voire kuma ta yi karin bayani a kan halin da ake ciki a garin Abobo

Ta ce ma'aikatan hukumar sun samu damar magana da wasu mutanen da suka tsere, sun yi magana a kan harbe harben bindigogi a koyaushe.

Kuma sun kasa yin barci sakamakon harbe harben bindigogin da suke ji.