Shugaba Chavez ya yi tayin shiga tsakani a Libya

Shugaba Chavez na Venezuela
Image caption Sasantawa tana da wuya

Kotun sauraran miyagun laifufuka ta duniya a Hague ta sanar cewa za ta gudanar da bincike kan miyagun laifufukan da suka saba wa dokokin kare hakokin biladama kan shugaban Libya Moummar Gaddafi da kuma mukarabansa a fadan da suke da masu zanga zanga.

Baban mai shigar da kara na kotun, Luis Moreno Ocampo , ya bayyana sunayyen Kanar Gaddafi da 'yayansa maza da kuma shugabannin wasu hukumomin tsaro na kasar.

Ya ce yana son ya sanar da su cewa kotun za ta dora alhaki a kansu idan har dakarun dake karkashinsu sun aiwatar da miyagun laifufka.

A kan rikicin na kasar Libya ne shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez, ya nuna sha'awararsa ta shiga tsakanin wadanda rikicin kasar Libyar ya shafa, don a warware abin cikin ruwan sanyi.

Libyar dai ta goyi bayan tayin, haka ita su ma kasashen Larabawa. Sai dai 'yan adawa suna adawa da abin, suna cewa an makaro saboda yawan zubar da jini da aka yi.