An kai harin bom a taron siyasa a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Ba a ba da labarin kama kowa ba

Hukumomi a jihar Neja sun tabbatar da matuwar mutane uku, tare da jikkatar wasu mutanen ashirin da takwas, bayan fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne a wani gangamin siyasa na jam'iyyar PDP a garin Suleja.

An ce, wasu mutane ne a cikin mota suka jefa bom din a wurin taron, suka kuma ranta a na kare.

Lamarin ya auku ne bayan da gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya kare jawabi a wata makaranta a garin na Suleja.

Ba a dai ba da labarin kama kowa ba zuwa yanzu.