Kotun hukunta manyan Laifuka za ta binciki Gaddafi

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Babban mai shigar da kara na Kotun manyan laiffuka, Luis Moreno Ocampo.

Babban mai gabatar da kara na kotun tuhumar manyan laifuka ta duniya, Luis Moreno-Ocampo, ya tabbatar cewar ofishinsa zai soma wani bincike kan laifukan cin zarafin jama'a a Libya.

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta laifukan yaki ta duniya Luis moreno Ocampo ya tabbatar da cewa ofishin nasa zai fara bincika zargin da ake yi wa gwamnatin Shugaba Gaddafi na Libiya na keta haddin biladaman kasar, wadanda ake zargin an aikata a lokacin rikice-rikicen bayan nan da ke aukuwa a kasar ta Libiya.

"Muna son mu sanar da ku cewa, yau uku ga watan Maris, na shekarar 2011, ofishin mai shigar da kara ya zartar da bude bincike kan zargin aikata laifukan keta hakkin biladama da aka aikata tun daga 15 ga watan Fabrairun shekarar nan. "

Ocampo ya ce bangarori biyu da suka hadar da gwamnati da kuma masu adawa da ita za a bincika a kuma hukunta su.

"Muna da bayanan da ke nuna cewa, bangaren 'yan adawa ma na dauke da makamai."

Ocampo ya kuma kara dacewa, "Ina son in bayyana karara cewa, idan 'yan adawa sun aikata laifukan yaki, su ma za mu bincike su. Ba za mu nuna bangaranci ba."

Mr Ocampo ya kuma bayyana sunan mutanen da ofishin nasa zai bincika wadanda suka kunshi shugaba Muammar gaddafi, da mukarrabansa da suka kunshi wasu daga cikin 'yayansa.

Jawabin na Mr Ocampo ya zo ne bayan da sojojin saman Libyan suka kai sabbin hare-hare a kan garin Brega da ke gabashin kasar.