An tarwatsa masu zanga-zanga a Libya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga zanga a Libya

Rahotanni daga Libiya sun ce, dakarun tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a birnin Tripoli, domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar neman ganin bayan jagoran kasar Kanar Muammar Gaddafi.

Wasu rahotannin kuma na cewa, fada ya barke a wajen babban birnin.

Haka ma, an ce an kara samun tashe-tashen hankula a gabashi da yammacin kasar ta Libiya.

Yanzu haka ministan Burtaniya mai kula da cigaban kasashe, Andrew Mitchell, yana ziyara a yankin iyakar Libiyar da Tunisia, domin ganin halin da dubban 'yan gudun hijira ke ciki.

Rikicen dai ya sake barkewa ne a Babban birnin kasar Libya wato Tripoli, bayan kammala salllar juma'a duk da baza dakarun da aka yi don kaucewa hakan.

Daruruwan mutane ne daga Tajura dake wajen garin Tripoli suka bi sahun masu zanga-zangar, garin da dakarun Kanal Gaddafi suka fuskanci kalubale a baya-bayan nan.

Garin dai shi ne yafi daukar hankali, saboda masu ganin bakin gwamnati da ke cikinsa, domin a da mafi yawan mazaunansa masu goyon bayan shugaba Gaddafi ne.

Sabon fadan dai ya barke ne a yayinda wasu hotunan tauraron dan adam ke nuna cewa dubban mutane ne 'yan Libya dake kokarin tserewa daga kasar sun makale kafin su isa bakin iyaka.

Ministan Burtaniyar mai kula da ayyukan cigaba na kasashen waje, Andrew Mitchell ne ya bayyana haka a lokacin da yake rangadi a wani sansanin 'yan gudun hijira dake dauke da 'yan Libya dubu goma sha takwas a Tunisia.

"Wannan wani yanayi ne mai cike da rashin tabbas." In ji Mitchell

"Da ya daga cikin matsalolin da ke akwai ta fuskar bada agaji shi ne ba mu da masaniyar mutane nawa ne za su samu karasowa bakin iyakar nan da kwana daya ko biyu ko uku masu zuwa, hotunan da tauraron dan adam ya dauko sun nuna cewa akwai mutane da dama a kilomita goma sha biyar kafin bakin iyakar wadanda ke son ketarowa." Sai dai ya bayyana cewa kyakkyawar halayyar mutanen Tunisia ya sa an kaucewa fadawa wani mummunan halin bukatar agaji.