Obama ya nemi Gaddafi ya yi murabus

Shuugaba Obama Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Shuugaba Obama ya ce Amurka ta damu da halin da ake ciki a Libya

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake yin kira ga shugaban Libya Mu'ammar Gaddafi da ya yi murabus. Mr Obama ya ce yana nazarin matakan da zai dauka kan rikicin da aka shafe makwanni uku ana yi.

Shugaban na magana ne a wani taron manema labarai a fadar White House tare da shugaban Mexico Felipe Calderon, wanda ya je Amurkan domin tattauna wa.

Wannan ba shi ne karo na farko da shugaba Obama ke neman Colonel Gaddafi ya yi murabus ba, a makon da ya wuce fadar White House ta yi hakan a rubuce, a yanzu kuma Mr Obama ya fada a taron manema labarai da aka watsa ta gidan talabijin.

Wani bangare ne na matsin lambar da Amurka ke kara yi kan shugaba Gaddafi.

Obama ya kara da cewa ya umarci ma'aikatar tsaro da kuma ta harkokin waje, da su fito da matakin da Amurka za ta dauka cikin gaggawa idan lamarin ya ci gaba da kazanta.

Shugaban na Amurka bai yi magana kai tsaye a kan batun hana zirga-zirgar jiragen sama a samaniyar kasar ta Libya ba, amma ya ce duk matakin da Amurka za ta dauka, zai kasance wani bangare ne na yunkurin kasashen duniya.