Libya ta nada sabon jakada a Majalisar Dinkin Duniya

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Kanar Gaddafi na magana ta gidan talabijin

Kasar Libya ta nada sabon jakada a Majalisar Dinkin Duniya bayan da jakandan na ta ya bujirewa gwamnatin shugaba Gaddafi.

Sai dai sabon jakadan bai isa Amurka ba, kuma babu tabbas ko zai samu izinin shiga kasar.

Wakiliyar BBC ta ce Nadin Ali Abdussalam Treki wani yunkuri ne da shugaba Gaddafi ke yi na dawo da tasirinsa a Majalisar ta Dinkin Duniya, wanda ya gurgunce a hannun jakadun da suka sauya sheka.

Gwamnatin Gaddafi dai na ikon sauya jakadan bisa, tun da dai har yanzu ita ce halattacciyar gwamnatin da ke wakiltar kasar ta Libya a Majalisar.

Sai dai babu tabbas ko Mr Treki zai samu damar shiga birnin New York domin fara aiki - hakan dai ya dogara ne kan mahukuntan Amurka za su bashi izinin shiga kasar ko kuma a'a.

Sai dai mataimakin jakadan na Libya wanda ya sauya sheka Ibrahim Dabashi, ya shaida wa BBC, jagoransa shi ne ke aiki har yanzu a Majalisar.

Shi ma mai magana da yawun Majalisar ya bayyana lamarin da cewa yana cike da rudani.