Karin zanga-zanga a kasashen Larabawa

Zanga-zanga a kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kasashen Larabawa na fuskantar wani yanayi mai cike da hadari

A yayin da hankali ya karkata kan kasar Libya, ana ci gaba da bore a wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika.

A Bahrain inda masu zanga-zanga suka bijirewa jami'an tsaro, 'yan adawa na ci gaba da matsawa gwamnati lamba.

Sun ce dai a shirye suke su tattauna da gwamnatin Sarki Khalifa, amma suna bukatar a kawo karshen mulkin kama-karya na 'yan dangi guda nan take. A Masar, zanga-zanga ta tilastawa Fira Minista Ahmed Shafiq yin murabus, yana daga cikin mukamai na karshe da shugaba Hosni Mubarak ya nada kafin ya bar mulki.

A farkon makwan nan ne kuma Fira Ministan Tunisia ya mika wuya, inda ya yi murabus bayan da masu zanga-zanga suka matsa kaimi.

Ana kuma ci gaba da zanga-zanga a kasashen Yemen da Oman, yayin da a Jordan ma, 'yan adawa ke ci gaba da neman sauyi.

Da dama daga cikin shugabannin yankin dai sun mai da martani ta hanyar daukar matakan saukaka wa jama'a halin kuncin da suke ciki.