An rufe Ofisoshin ACN a jihar Ribas

Jam'iyyar ACN reshen jihar Ribas ta zargi gwamnatin jihar da sawa a kulle ofisoshinta na kamfen a dukan fadin jihar.

Dan takarar gwamnan ACN din a jihar Chief Abiye Sekibo, ya zargi gwamnatin jihar, ta PDP, da daukar matakin ne, saboda tana ganin cewa zai kada ita a zabe mai zuwa.

Amma a nata bangaren, gwamnatin Ribas din ta ce an kulle ofisoshin ACN ne, saboda rashin biyan kudaden haraji.

Wannan lamari dai ya soma janyo zaman dar-dar tsakanin magoya bayan bangarorin biyu.