Mahaka ma'adinai a Afirka ta Kudu sun yi nasara a kotu

Jacob Zuma, Shugaban Afirka ta Kudu
Image caption Jacob Zuma, Shugaban Afirka ta Kudu

Kotun kolin Afrika ta Kudu ta yanke hukuncin cewa, masu aikin hako ma'adinai dake fama da ciwon huhu, suna iya shigar da karar kamfanonin da suke yiwa aiki.

An kiyasta cewa ma'aikata dubu 280 ne dake aikin hakar zinare a yankin Kudancin Afrika ke fama da ciwon huhu, a sanadiyyar kurar da suke shaka a wuraren aikinsu.

Ma'aikacin da ya shigar da karar ya rasu, amma kamfanin da yayi wa aiki, AngloGold Ashanti, ya amince da hukuncin.