ACN ta wanke kanta kan batun kawance da CPC

Image caption Malam Nuhu Ribadu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyar ACN

A Najeriya, yayin da ya rage kasa da wata guda a gudanar da babban zaben kasar, jam'iyar adawa ta ACN ta ce ko kadan bata laifi na rashin cimma matsaya game da batun kawance tsakaninta da jam'iyar CPC.

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar, Malam Nuhu Ribadu, ya ce jam'iyar sa tayi iyakacin kokarinta na ganin ta kulla kawance da jam'iyar CPC, amma abin ya ci tura.

Haka zalika, Jam'iyyar ta Action Congress of Nigeria, ACN, ta ce babu wata jam'iyya da zata iya karbe Jihar Lagos daga hannunta. Jam'iyyar ta bayyana haka ne a lokacin gabatar da wasu daga cikin 'yan takarar ta wadanda suka hada da Malam Nuhu Ribadu, dan takarar shugaban kasa, da kuma Cif Babatunde Fashola, dan takarar gwamnan jihar Lagos.