Saudiyya tayi gargadi akan zanga- zanga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdallah na kasar Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya tayi gargadi akan gudanar da duk wani irin zanga- zanga a kasar, inda ta ce yin haka haramtacce ne kuma ya sabawa addinin Islama.

Gwamnatin Saudiyyar ta ce jami'an 'yan sanda zasu dauki `kwakkwaran mataki akan duk wasu da suka nemi su karya doka.

Ma'aikatan harkokin cikin gida ta kasar ta fitar da wannan gargadin ne, bayan wani karamin zanga zanga da aka gudanar a wani yanki da 'yan Shi'a ke da rinjaye a gabashin kasar.

An dai yi ta kiraye kirayen da a gudanar da zanga a watan nan don neman ayi sauye sauye ta fuskar siyasa.