CPC na korafi kan kama Sanata Dan Marke

A Nijeriya, yayinda 'yan siyasa ke cigaba da yakin neman zabe, zaman zullumi na dada karuwa a jihar Katsina bayan da dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC Senata Lado Dan-marke ya shafe kwanaki biyu a hannun 'Yan sanda.

Rundunar 'yan sandan na zarginsa da tunzura magoya bayansa su yi ma gwamnan jihar Ibrahim Shehu Shema ihu.

Rahotannin da muka samu sun ce, kama Senata Dan-marken ya haddasa rudani da zanga-zanga da kone-konen tayoyi a duk tsawon jiya a birnin na Katsina.

Hukumomi sun ce a gobe zasu gurfanar da shi a gaban kotu.