Ban yi nadamar abinda na yi ba-Sheikh Abubakar

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya na da mabiya addinai da kabilu daban-daban

A Najeriya Sheikh Abubakar Jibril limamin masallacin juma'a na Farfaru dake birnin Sokoto, ya ce rashin cika alkawari ne ya sa shi yin adawa da takarar shugaba Jonathan.

Sheikh Abubakar ya zargi shugaba Jonathan da laifin karya tsarin nan na karba-karbar mulki tsakanin Kudu da Arewacin kasar na jam'iyyar PDP.

Malamin wanda 'yan sanda suka kama bisa shafawa allunan hoton shugaba Goodluck Jonathan bakin fenti a Sokoto ya shaida wa BBC cewa ko kadan, bai yi nadamar abinda ya yi ba.

Da yammacin ranar Asabar ne dai Sheikh Abubakar Jibril ya koma gidansa bayan 'yan sanda sun sako shi da maraicen juma'a.

Ranar Litinin din da ta gabata ne dai 'yan sanda suka kama malamin bisa zargin kokarin ingiza wutar rikici ta hanyar jagorantar wasu ya'yansa da kuma wasu mukarrabansa wajen shafawa allunan hoton shugaba Goodluck Jonathan bakin fenti.

Daga nan ne kuma suka wuce da shi birnin tarayya Abuja, domin yi masa tambayoyi.

Malamin ya ce Hukumar 'yan sandan ta ajiye shi a wani wuri da yace anan ne ake ajiye masu manyan laifuka.