Tsohon Shugaban Faransa zai gurafana a kotu

Jacques Chirac Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon hugaban Faransa Jacques Chirac

Idan an jima a yau ne ake sa ran tsohon Shugban Faransa Jascques Chirac zai gurfana a gaban kuliya a birinin Paris bisa zargin yin sama da fadi da kudaden gwamnati a lokacin da ya rike mukamin Magajin Garin Paris.

Ana zargin Mista Chirac da amfani da asusun gwamnati domin samar da ayyuka ga wadasu ‘yan siyasa wadanda suka taimaka masa wurin tsayawa takarar shugaban kasar da aka gudanar a 1995 wanda ya lashe.

A karkashin dokokin kasar Faransa dai ba dole ba ne ga tsohon Shugban kasar ya gurfana a gaban kuliya, amma ana sa ran Mista Chirac zai bayyana gobe Talata.

Yanzu haka dai shekarun Mista Chirac saba’in da takwas kuma yana fama da rashin lafiya.