Gaggan 'yan siyasa sun yi rajista fiye da daya

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben Nigeria, wato INEC, ta ce za ta gurfanar da duk wadanda aka gano cewa sun yi rijista fiye da sau daya a rijistar masu kada kuria'a da aka kammala a kwanakin baya.

Hukumar zaben ta kuma ce ta gano cewa akwai wadansu gaggan 'yan siyasa wadanda suka yi rijista fiye da sau daya, kuma nan ba da jimawa ba za su gurfana a gaban kuliya.

Kakakin hukumar, Mista Nick Dazang, ya shaidawa BBC cewa, “Akwai jiga-jigan ‘yan siyasa ma wadanda aka tarar sun yi rijista fiye da daya”.

Ko da ya ke Mista Dazang ya ce ba zai bayyana sunayen wadannan ‘yan siyasa a yanzu ba, ya ce daga yanzu zuwa lokacin da za a gudanar da zabe za a gurfanar da zu a gaban kotu.

Korafe-korafe da dama ne dai suka dabaibaye aikin rijistar masu kada kuri'ar da hukumar zaben ta gudanar.