'Alkalan Kotun Kolin Najeriya sun Karbi Cin Hanci' - In ji Bankole

Image caption Dimeji Bankole, Kakakin Majalisar Wakilan, Najeriya

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Dimeji Bankole ya maida martani cikin fushi game da bayanan da jaridar Next ta wallafa cewa alkalan kotun kolin Nigeria sun karbi cin hanci a shari'ar da suka gudanar na zaben shekarar 2007.

Martanin kakakin majalisar wakilan Najeriyar, na zuwa ne bayanda jaridar ta Next ta ce ta samu wasu bayanai daga shafin nan mai kwarmata bayanai na Wikileaks, wanda ke cewa alkalan sun karbi hancin ne domin baiwa marigayi Alh Umaru Musa Yar'adua da mataimakinsa Dr Goodluck Jornathan a wancan lokacin nasarar zaben na 2007.

A wata Sanarwa mai dauke da zafafan kalamai dake cewa, kakakin majalisar Dimeji Bankole ya musanta da babbar murya cewa ya taba yin wannan zargi akan alkalan kotun kolin.

A cewar jaridar dai, kakakin majalisar dokokin ne ya shaidawa tsohuwar jakadiyar Amurka a Najeriya Ms Robin Sanders, cewa yana da shaidu kan cin hancin da wasu alkalan kotun kolin kasar suka karba daga wurin tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori wanda a halin yanzu yana tsare a gidan yarin Dubai.

A cewar jaridar, kakakin majalisar ya sadu da jakadiyar Amurkan ne a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2007, inda ya shaida mata cewa yana da kwararan shaidu dake nuna cewa alkalan sun karbi hancin ne domin baiwa marigayi Alh Umaru Musa Yaradua da mataimakinsa na wancan lokaci Dr Goodluck Jonathan nasara a zaben shekarar 2007, wanda masu sa ido na cikin gida da na waje suka ce yana cike da kura-kurai.

A sanarwar, kakakin majalisar wakilan ya ce, ba boyayyen abu bane irin abotar dake tsakanin marigayi Alhaji Umaru Musa Yaradua da shi, baya ga cewa yana tare da gwamnatinsa.

Don haka a cewar sanarwar, hankali ma ba zai dauka ba, yadda duk da wannan abota zai yi kalamanda za su yi zagon kasa ga mulkinsa. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bai kamata duk wata kafar yada labaru ta wallafa abinda karara babu gaskiya a ciki ba, wanda kawai rade-radi ne kawai.

A karshe sanarwar ta ce, kamata yayi kafafen yada labaru su rika tantance bayanai kafin su wallafa, ba kawai duk wata shara za su dauka su wallafa a jaridunsu ba, domin kare mutuncin ma'aikatar shari'ar kasar wadda ita ce matakin karshe na samun adalci ga talaka.