Rikicin Libya na ci gaba da ruruwa

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Libya ta amince ta bar wata tawagarta ta shiga cikin kasar domin duba halin da jama'a ke ciki.

Ana dai ci gaba da gwabza mummunan fada a Gabashi da Yammacin kasar Libya yayinda sojojin da ke biyayya ga Kanar Gaddafi ke yunkurin kwato yankunan dake hannun 'yan tawaye.

Abin da ake gani na kama da yakin basasa a kasar Libya, ya kasance wani rikici da ba kasafai ake ganin irinsa ba, a saboda su kansu kungiyoyin agajin bil adama basu da wata rawar a zo a gani da zasu iya takawa a kasar.

Kasancewar soji a kasa ya kara sanyawa da wuya a fuskanci hakikannin lamarin.

Sai dai kuma abubuwan dake faruwa a manyan garuruwan kasar sun sanya damuwa a bangaren kasashen duniya kan cewa akwai yiwuwar rikicin ya ci gaba da ruruwa.

Shaidu wadanda suka ji ko suka gani dai na da matukar mahimmanci idan har ana so a iya auna halin da bil adama ke ciki a kasar, sannan kuma akwai bukatar damar aikewa da agajin magunguna zuwa wuraren da ake bukatar su.

Rashin sanin hakikanin gaskiyar abinda ke akwai ta sa fuskantar lamarin ya kasance mai kamar wuya.

Shugabar hukumar kai daukin gaggawa ta majalisar dinkin duniya Valerie Amos ta yi misali da garin Misrata dake yammacin kasar inda aka tafka kazamin rikici, inda ta yi nuni da cewa kungiyar agajin kasa-da-kasa ta Red Cross ta taimaka matuka.

Tace a bangaren yamma, wato wuraren da ake yawan ganin mutane ta akwatin talabijin na tafka kazamin rikici, sannan kuma a Benghazi kungiyar agajin Red Cross da kuma reshen kasar Libyan sun taimaka da kayan agaji da kuma motocin kai dauki.

Dr Ahmed Sewehli wani likita ne dan Libya dake aiki a Ingila, wanda ya bar aikinsa domin komawa Libya don agazawa:

Yace "A jiya Lahadi na gana da abokan aikina dake asibitin Misrata wadanda suka shaida min cewa an kai musu hari. Mutane ashirin sun rasu, yayinda chasa'in da hudu suka ji rauni, kuma mafi yawansu raunin a ka suka ji ko a kirjinsu ko a baya. Abin takaicin shi ne babu ma'aikata da yawa da zasu iya da wadanda suka ji munanan raunuka.

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon dai ya bayyana cewa jami'an kasar Libya sun amince da wata tawaga ta masu sa ido akan halin da bil adama ke ciki, sai dai zasu fara ne da babban birnin kasar Trabulis wato Tripoli.

An dauki matakan sakawa Libya takunkumi da kuma gurfanar da kasar a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ba don komai ba sai don tunanin nan ba da jimawa ba Kanal Gaddafi zai saduda ya bada kai bori ya hau.

Sai dai kasancewar har yanzu bai sauka ba, kuma bashi ma da niyyar yin haka ya sake zafafa rikicin da ake yi wanda ka iya sawa da wuya duka bangarorin su iya yin nasara.