Rikice-rikice a Afrika na da nasaba da siyasa

Hakkin mallakar hoto AP

Masana sun bayyana cewa mafi yawan rikice-rikicen da ake fama da su a nahiyar Afirka na da nasaba da siyasa da kuma tattalin arziki.

A cewar masanan matukar ba a samu daidaito ta fuskar rabon tattalin arziki da kuma adalci ta bangaren shugabannin jama`a ba, da wuya a samu zaman lafiya a nahiyar.

Masanan sun yi wannan hasashen ne a wajen wani taron da gidauniyar African Peace Foundatin ta shirya a Abuja.

Kasashen Afirka da dama ne ke fama da rigingimu, cikinsu har da Somalia da Darfur da Ivory- Coast da kuma Najeriya.

Masanan sun bayyana cewa irin guguwar sauyin da take kadawa a kasashen larabawan da ke bangaren arewacin Afirka da kuma rikicin da ake fama da shi a Darfur da Somalia sun isa a kafa hujjar cewa akasarin rikice-rikicen nahiyar sun fi nasaba da siyasa da kuma tattalin arziki.

Kuma sai shugabannin kasashen sun sauya salon jagoranci kafin zaman lafiya ya dawwama a wadannan wuraren.

Dr Yakubu Musa jami`i a gidauniyar kyautata zaman lafiya ta African Peace Foundation a Najeriya, ya ce jinkirin da mahukuntan kasar ke yi wajen aiki da shawarwarin da ake ba su shi ne dalilin da ya sa wutar rikice-rikicen ta ki mutuwa.

Ita ma Najeriya tana fama da wasu rikice-rikice da suka-ki-ci-suka-ki-cinyewa a wasu jihohin kasar.

Alal misali, jihar Borno ta yi kaurin-suna da rikicin boko-haram, yayin da jihar Pilato ke fama da rikicin kabilanci da siyasa, da kuma tattalin arziki, wadanda suka yi sanadin asarar dubban rayukan jama`a da dukiya.

Masanan dai na jaddada cewa zaman lafiya ginshiki ne ga ci gaban kowace al`umma, don haka kasashen nahiyar Afirka da dama na da babban kalubale a gabansu na shawo kan rigingimun da suke fama da su kafin su kai ga cimma burinsu na samun habaka da bunkasa.