Ana cikin tsaka mai wuya a Abidjan

Tashin hankali a Abidjan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tashin hankali a Abidjan

Akalla mutane 4 sun hallaka a lokacin wata zanga zanga a birnin Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar Cote d'Ivoire.

Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sun ce maza uku da mace daya ne sojojin dake goyan bayan Laurent Gbagbo, mutumin da ya ki sauka daga kan mulki, suka bindige.

An kashe su ne bayan da wasu daruruwan mata suka yi maci a Abidjan, domin kokawa da kisan da aka yiwa wasu mata 7, a lokacin wata zanga zanga a makon da ya gabata.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 400 ne aka kashe tun bayan rikicin da ya barke akan zaben shugaban kasar na shekarar da ta wuce, wanda ake takaddama a kansa.