An gurfanar da dan takarar CPC bisa zargin dana bam

Mahukunta a Najeriya sun gurfanar da dan takarar kujerar Majalisar dokoki a Sulejan jihar Naija a gaban kuliya, bisa zarginsa da shirya harin bam din da aka kaddamar a Suleja a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mutane uku suka rasa rayukansu a harin a yayin da akalla mutane ashirin da takwas su ka jikkata.

An gabatar da dan takarar Mallam Abdullahi Lado a Kotu ne, bisa zarginsa da shirya kisa da kuma raunata mutane.

Dan takarar ya musanta zargin, inda ya ce an kitsa zargin ne da manufar siyasa.

An dai zargi dan takarar ne da wasu mutane hudu, wadanda ba'a kai ga kama su ba, kuma ana zaton sun tsere.

Alkalin Kotun Muhammed Tanko ya dage sauraran karar zuwa ranar 18 ga watan Afrilu, amma ya umarci hukumar tsaron farin kaya ta SSS da ta ci gaba da tsare dan takarar har sai an saurari karar.

Kakakin dan takarar Shugaban kasa na Jam'iyyar CPC Mista Yinka Odumakin ya yi watsi da zargin da ake yi wa dan takarar jam'iyyar, inda ya zargi jam'iyyar PDP da kitsa zargin saboda manufar siyasa.