Cutar amai da gudawa na kisa a Kaduna

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

An sami sami barkewar annobar amai da gudawa a Kaduna, wadda ake kyautata zaton cutar kwalara ce.

Rahotanni daga sassan garin Kadunar, kamar su Barnawa da Kawo sun nuna cewa, cutar ta kama mutane da dama, wadanda a yanzu ke kwance a asibitoci.

Kimanin mutane hudu ne suka rasu a Barnawa, daya daga cikin yankunan jahar da wannan cuta a yanzu ta zame wa annoba.

Lokaci zuwa lokaci ana fama da amai da gudawa a wasu sassan Najeriyar.

Rashin tsabtar muhalli da ruwa marar tsabta na daga cikin abubuwan da ke haddasa cutar.