Gubar dalma na kara yin illa a Najeriya

Aikin rufe gubar dalma a Zamfara
Image caption Aikin rufe gubar dalma a Zamfara

A Najeria rahotanni sun ambato hukumar samar da agajin gaggawa ta kasar, wato NEMA, tana cewa wadansu karin yara dari hudu sun mutu a arewacin kasar sanadiyyar dalma mai guba tun watan Nuwamban bara.

Wannan adadi na nuni da cewa, yawan wadanda suka rasu sakamakon mu'amala da dalmar a Jihar Zamfara na karuwa.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce mutane kimanin dari hudu ne suka rasu a jihar ta Zamfara daga watan Maris zuwa watan Oktoban bara.

Masana sun yi gargadin cewa yanzu kusan duk fadin kasar na fuskantar barazanar wannan mugun sinadari na dalma.

A cewar Dokta Sani Gwarzo, wani jami’i a Cibiyar Yaki da Cututtuka da ke Amurka, “A ko wacce jiha da za ka zagaya a Najeriya, akwai wasu abubuwan da akan yi da su kan kara yaduwar gubar dalma.

“Duk jihar da ake amfani da tsohon batiri na mota, ana fasa shi ana sake amfani da robar, to duk kewayen inda aka yi aikin da wadanda suka yi, da iyalansu da inda suka je suka yada wannan ruwan batir din yana kara gubar dalma.

“Sannan duk inda ake da tsohon talabijin irin mai zumbutun nan, ko irin kwamfiyuta mai zumbutun nan na baya suna dauke da sinadarin dalma mai tsananin yawa; da [sun] gama aiki an ya da [su sun] fashe, to za [su] saki wannan guba a wannan wuri.

“…Duk wanda ya ke kewaye da wannan wurin—tun daga kasar wurin har kurar wurin, har inda idan ruwa ya kwaranyar da ruwan ya shiga kogi ko ya shiga rijiyoyin mutane, akwai gubar dalma a wannan wuri”.

Dokta gwarzo ya kuma ce yawan mace-macen da aka gani a Jihar Zamfara ka iya faruwa a wadansu sassa na Najeriya, to amma, “ba za a iya ganinsa ta sauki ba”.

“Sai dai illarsa ta rika bayyana, matsalarsa ta rika bayyana—wani ma ba za a gane gubar dalma ba ce.

“Illolinta da dama: akwai yawan ma’auni a cikin jini—musamman ga yara—idan ya kai yaran za su mutu.

“Akwai kuma wanda idan ba su mutu ba, to za su zama cikin dawamammen rashin cikakken kaifin kwakwalwa; za su zama wawaye, dolaye, sannan ba sa iya daukar karatu.

“Sannan wasu daga cikinsu su kan samu tabin hankali ma su yi hauka, ko kuma sassan jikinsu su shanye.

“Sannan manya za su iya samun rashin karfi—musamman na ma’aurata—kuma ya zamana an samu yawan bari ga mata, da kuma rashin haihuwa”.

Dokta Gwarzo ya kuma ce matakan shawo kan matsalar a matakan gwamnatin tarayya da jihohi sun hada da kirkiro wani sashe wanda zai rika kula da wannan matsala, da kuma samar da tsari na zubar da sharer kayayyakin laturoni musamman batura da talabijin da kwamfiyuta.