Kasashen duniya na kara goyon bayan hana jiragen saman yaki shawagi a samaniyar Libya

Sakatare janar na kungiyar kasashen Musulmi ta duniya ya ce yana goyan bayan hana jiragen saman libya shawagi a sararin samaniyar kasar domin hana Kanar Gaddafi kaiwa abokan hamayyarsa hari ta sama.

Da yake magana a wajen wani taron gaggawa na mambobin kasashen kungiyar 57, Ekemeleddin Ihsanoglu,ya ce, kamata yayi kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yayi aikinsa.

Amma dai ya ce bai yadda da daukar matakin soji ba. Wakilin BBC yace hana shawagin jiragen sama na libya a sarararin samaniyar kasar tamkar kawadda dakarun saman Gaddafi ne daga filin daga.

A filin daga kuma dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi sun sake kai hari ta sama a garin RasLanuf dake da mai a gabashin Libya.

Wadanda suka ganewa idanunsu abinda ya faru sun ce an kai daya daga hare haren ta sama kan wata unguwa da mutane ke ciki, inda a kai raga raga da wani gini mai hawa biyu.

Da alama an kwashe mutanen da ke gidajen da aka kai harin, kuma ba wani da aka ce ya samu rauni.

Har yanzu dakarun Kanar Gaddafi na ci gaba da kewaye garuruwan Zawiya da Misrata dake hannun 'yan tawayen, inda rahotanni ke cewa ana kai hari da manyan bidigogin Igwa garin Zawiya.